<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Yesu Yana Bakin Ƙofa LW151</title>
<lyrics>[V1]
 1) Yesu yana bakin ƙofa,
 Yana ta da murya,
 Ku ƴan Adam duk, ku ji ni,
 Shiga ƙofar hanyata.

[V2]
 2) Ƙofan nan da wuyar shiga
 Hanya kuwa ƙunƙunta ce,
 Masu shiga babu yawa,
 Sai mutane kima ne.

[V3]
 3) Dukan masu son adalci,
 Dukan masu ƃacin rai,
 Masu ladabi a ruhu,
 Su ke shiga, su kaɗai.

[V4]
 4) Ba da dukiya za mu je ba,
 Ba kuwa da aniya ba,
 Ba don aikin nagarta ba,
 Sai da bangaskiya kaɗai.

[V5]
 5) Wata ƙofa tana nan kuwa,
 Masu shiga sun yi yawa,
 Hanyan nan kuwa ke da fādi
 Za ta kai su halaka.

[V6]
 6) Hanyan nan da sauƙi ta ke,
 Gama babu kokawa
 Da jaraba ko mugunta,
 Ba kuwa masu hanawa.

[V7]
 7) Ba su ganin inda za su,
 Ba tsammanin halaka.
 Duniya duk da ruɗin Shaiɗan
 Su kan rufe idonsu.

[V8]
 8) Tashi, masu laifi duka,
 Sai ku nemi gafara,
 Sai ku karƃi kyautar Allah
 Sai ku riƙa yin godiya.</lyrics>
<hymn_number>151</hymn_number>
</song>